Karanta rubutu kawai domin rage cin data Asalin hoton, Getty Images An wallafa Sa'o'i 4 da suka wuce Lokacin karatu: Minti 4 Babban Bankin Najeriya ya ce matsin lambar da ake fuskanta a ƙasar a kasuwar canjin kuɗaɗen waje ya ragu matuƙa, yayin da ajiyar kuɗin waje ta ƙasar ta ƙaru zuwa dala biliyan 55.25. Haka nan rarar asusun hada-hadar ƙasashen waje ta Najeriya ta ƙaru da kashi 67.92, inda dadin ya ta tashi zuwa dala biliyan 7.54 a zangon watanni uku na biyu na shekarar 2026. An bayyana alƙaluman ne a cikin sanarwar taron kwamitin tsara manufofin kuɗi na Babban Bankin Najeriyar, CBN , wato taronsa na 307, wanda aka gudanar ranar Talata.
Kwamitin ya ce ƙarfafa tushen tattalin arzikin Najeriya a hulɗarta da ƙasashen waje da kuma ƙarin amincewar masu zuba jari na daga cikin abubuwan da suka taimaka wajen wannan ci gaba. Matakin rage kuɗin ruwa A yayin taron, CBN ya rage babban kuɗin ruwa daga kashi 26.5 zuwa kashi 23, domin sake tsara manufofin kuɗi da kuma daidaita tsarin iyakar kuɗin ruwa na bankin. Haka kuma, rarar ma'aunin biyan kuɗaɗen ƙasa da ƙasashen waje, ta ƙaru daga dala biliyan 2.38 zuwa dala biliyan 3.51 a cikin wannan lokaci.
Bankin ya ce ingantuwar matsayin Najeriya a harkokin kuɗaɗen waje ta taimaka wajen ƙara daidaiton kasuwar canjin kuɗin waje. Da yake magana bayan taron, Gwamnan CBN, Olayemi Cardoso, ya ce matsin lambar canjin kuɗin waje ya ragu matuƙa, yayin da Najeriya ta sake gina ajiyar kuɗaɗenta na waje. Ɓangarorin da cigaban ya shafa Akwai ɓangarori da dama da gwamnatin Najeriya ta ce ta samu ci gaba a bunƙasar tattalin arzikinta, ga wasu daga sassan da gwamnatin Najeriyar ta bayyana an samu bunƙasar a zahiri: Ajiyar kuɗin waje: Ta ƙaru zuwa dala biliyan 55.25 zuwa 18 ga Satumba 2026, matakin da CBN ya ce shi ne mafi girma cikin shekaru 18. Rarar asusun hada-hadar ƙasa da ƙasashen waje: Ta ƙaru da kashi 67.92, daga dala biliyan 4.49 a zangon farko na 2026 zuwa dala biliyan 7.54 a zangon na biyu.
Rarar ma'aunin biyan kuɗaɗen ƙasa da ƙasashen waje: Ta ƙaru daga dala biliyan 2.38 zuwa dala biliyan 3.51 a zangon watanni uku na biyu. Kasuwar canjin kuɗin waje: Matsin lambar da ake fuskanta a kasuwar canjin kuɗin waje ya ragu sosai, abin da ya taimaka wajen samun ƙarin daidaito a kasuwar tare da zama mai tasiri ga tattalin arzikin Najeriya. Kuɗaɗen da 'yan Najeriya ke turawa daga ƙasashen waje: Babban Bankin Najeriyar ya ce kuɗaɗen da 'yan ƙasar ke Aikawa gida sun taimaka wajen ƙarfafa ajiyar kuɗin waje da juriyar tattalin arzikin ƙasar.
Amincewar masu zuba jari: CBN ya ce ingantuwar matsayin kuɗin waje da samun daidaito a kasuwar canjin kuɗaɗen ƙeatare sun taimaka wajen ƙara amincewar masu zuba jari a kasuwannin kuɗi na Najeriya. A baya, CBN ya ƙaddamar da wasu matakai domin ƙara yawan kuɗaɗen da 'yan Najeriya ke turawa daga ƙasashen waje. Waɗannan tsare-tsare na bai wa 'yan Najeriya da ke zaune a ƙasashen waje damar turo kuɗaɗensu zuwa Najeriya da kuma sarrafa ko zuba jarin kuɗin a cikin ƙasar.
Gwamnan ya ce ingantuwar matsayin Najeriya a harkokin kuɗaɗen waje ta taimaka wajen ƙara daidaiton kasuwar canjin kuɗin waje, tare da dawo da amincewar masu zuba jari a kasuwannin kuɗi na ƙasar. A taron manema labarai CBN ya ce an yi sauyin ne domin ƙarfafa yadda manufofin kuɗi ke tasiri a tattalin arziki, tare da tabbatar da cewa tsarin ya kasance babban abin da ke nuna alkiblar manufofin kuɗin bankin. Tasirin tattalin arzikin ga 'yan ƙasa Masana tattalin arziki sun bayyana sanarwar gwamnatin kasar a matsayin babban alfanu inda sukace an samu aƙalla ƙaruwar adadin da ya kai 0.20 cikin ɗari, abin da Dakta Murtala Abdullahi Kwara malami a sashen nazarin tattalin arziki na Jami'ar Umaru Musa Yar aduwa da ke Katsina, ya ce kuɗaɗe ne masu yawa.
Masanin ya kuma ce, "an samu ci gaba ta wasu ɓangarori da suka haɗa da ƙaruwar kuɗaɗen shiga daga ɓangaren gwamnati, to sai dai wannan bunƙasar tamkar alƙalumman kan takarda ne kawai kuma ƙaruwa a ajiyar kuɗin waje da rarar asusun hada-hadar ƙasa da ƙasashen waje na iya nuna cewa wasu sassan tattalin arziki suna samun sauƙi, amma hakan ba ya tabbatar da cewa 'yan ƙasa sun fara samun sauƙin rayuwa", in ji shi. Asalin hoton, Getty Images Ƙaruwar masu saka jari Asalin hoton, AFP Bayanan hoto, Matatar man fetur Kazalika, a cewar Babban Bankin Najeriya daidaiton da aka samu a kasuwar canjin kuɗin waje ya taimaka wajen dawo da amincewar masu zuba jari a tattalin arzikin ƙasar. Gwamnan CBN, Olayemi Cardoso, ya ce raguwar matsin lambar canjin kuɗin waje da sake gina ajiyar kuɗin waje na Najeriya sun taimaka wajen inganta yanayin kasuwannin hannayen jari.
Ya ce ingantuwar kasuwar canjin kuɗin waje na daga cikin abubuwan da suka taimaka wajen ƙara kwarin gwiwar masu zuba jari, yana mai cewa abin da ake gani a kasuwannin jari na da alaƙa da daidaiton da aka samu a kasuwar canjin kuɗin waje. To sai dai Dakta Murtala Abdullahi Ƙwara, "waɗannan masu zuba jari daga waje da gwamnatin Najeriyar ke magana, kawai suna zuba shi ne a kasuwar cunku ba wai kamfanonin 'yan ƙasar da gwamnati suke zuwabawa jarin ba ta hanyar zuwa da kuɗi su buɗ kamfanoni da za su taimakwa 'yan ƙasar wajen samun aikin yi ba". Haka kuma masanin ya ce, suna zuba kuɗin ne na ɗan lokaci da sun ci riba sai su kwashe kuɗin su koma wasu ƙasashe na daban luma wannan na daga cikin ainihin abin da aka san waɗannan mutane da yi.
Amma a CBN ya ce ingantuwar matsayin Najeriya a harkokin kuɗaɗen waje na daga cikin abubuwan da suka bai wa kwamitin tsara manufofin kuɗi, MPC, ƙarin ƙwarin gwiwa wajen sake tsara tsarin manufofin kuɗin ƙasar. Yayin da gwamnati ke kallon waɗannan alkaluma a matsayin alamar cewa gyare-gyaren tattalin arziƙin na aiki, masana na cewa ainihin ma'aunin nasara shi ne yadda wannan ci gaba zai sauya rayuwar 'yan ƙasa. Wannan dai na daga cikin bayanan baya-bayan nan da gwamnatin shugaban Najeriyar Bola Ahmed Tinubu ke fitarwa domin nuna tasirin matakan ginin tatalin arziki da suka bayyana suna dauka duk kuwa da halin matsin da 'yan kasar ke cewa suna fama da shi.
Source: BBC
Texas · Hometown Post


